'Yan Kungiyar Boko Haram Sun Sace Fiye Da Mutane 300 A Jihar Borno

Yan bindiga

Yan bindiga

Rahotanni daga Ngala hedkwatar Gambarou Ngala a jihar Borno, na cewa 'yan kungiyar Boko Haram sun yi garkuwa da kimanin mutane 319.

WASHINGTON, D. C. - Bayanan daga wata majiya mai tushe ta bayyana cewa, mutane sun nuna damuwarsu matuka da wasu mata 319 da ‘yan ta’addan suka yi garkuwa da su, wanda ya nuna tsabar rashin tsaron lafiyar al’umma a yankunan da ake fama da rikici.

Da take tabbatar da sace mutanen, wata majiyar tsaro, wacce ta bukaci a sakaya sunanta, ta amince da sabanin da aka samu a alkaluman da aka bayar, wanda ke nuni da cewa an sace ‘yan gudun hijira kusan 113, sabanin adadin da ke yawo a cikin rahotanni.

Karin haske daga wata majiya a sansanin ‘yan gudun hijira na Babban Sansani ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Lahadin da ta gabata a lokacin da mata suka kutsa cikin daji domin dibar itacen amfanin cikin gida da kasuwanci, sai dai suka fada hannun maharan.

A cewar majiyar, ‘yan ta’addan sun kewaye su ne a dajin Bula Kunte da ke yammacin garin Ngala. Suka 'yantar da tsoffi suka shiga daji tare da 'yan mata 319 masu karfi da kuzarin jiki da wasu yara maza."

Da suke ba da labarin yadda suka tsere, wasu ‘yan mata uku da suka yi nasarar guduwa suka koma Ngala, sun ba da labarin yadda maharan suka kai su wani daji kusa da kauyen Bukar-mairam a jamhuriyar Chadi

"Muna gargadin su ko da yaushe da su kasance cikin wuraren da akwai tsaro, amma matsin tattalin arziki ne ya tilasta yawancinsu suka tafi da nisa.

“Ba su da wata hanyar rayuwa da ta wuce yankan itatuwa domin sayarwa. Ana siyar da ɗan ƙaramin garin masara akan Naira 2,200. A ina za su sami kuɗin da za su saya? Ba za mu iya hana su ba idan ba za mu iya ciyar da su ba. " in ji majiyar.

Wannan shi ne adadi mafi yawa da aka sace tun bayan kwashe ɗaliban sakandaren Chibok su 276, shekaru 10 da suka gabata.