Wakilin sashen Hausa a jihar Adamawa arewa maso gabashin Najeriya, Ibrahim Abdulaziz ya aiko da rahoton na cewa, 'yan yakin sa kan kungiyar Boko Haram sun sake kai wani hari a wasu yankunan Michika dake arewacin jihar Adamawa, inda suka kashe mutane da dama, tare da kona gidaje.
Wuraren da aka kaiwa harin sun hada da Shahu da Liddle da Gumchi da Garta da Kamale da kuma Mbororo.
Wani mazunin yankin yayi bayanin cewa yan Boko Haram sun kashe mutane da dama, yayinda dan Majalisar dake wakiltar mazabar Michika a Majalisar wakilan jihar Adamawa ya tabbatar da kai harin, inda yace yan kungiyar ta Boko Haram sun yiwa wasu mutane yankan rago, kuma suna ci gaba da kone kone. Ya roki gwamnati data kai doki.
Ya zuwa yanzu dai ba'a san adadin wadanda aka kashe da kuma wadanda aka sace ba.
Wani kusa a kungiyar maharba wadanda suke fagen daga ya shedawa Ibrahim cewa ana samun nasarar akan farmakin da ake kaiwa yan Boko Haram.
Jami'an tsaro basu ce komai gameda wannan harin ba, Kawo yanzu kananan hukumomi. Minchiga da Madagali na jihar Adamawa suna hannun yan Boko Haram.
Your browser doesn’t support HTML5