'Yan Kudancin Sudan Dubu 15 Zasu Bar Aikin Soja Yau Alhamis

Sojojin Kudancin Sudan su na maci na gwajin babban faretin da zasu yi ranar asabar, 9 Yuli, watau ranar da yankin zai zamo kasa 'yantacciya

A yayin da kudancin Sudan ke shirin zamowa 'yantacciyar kasa, sojoji 'yan asalin yankin zasu fita daga rundunar sojojin Sudan ta Arewa

Rundunar sojojin Arewacin Sudan tana tube ma dakaru dubu 15 ‘yan asalin Kudancin Sudan rigunansu na rundunar a yau alhamis, a daidai lokacin da Kudanci ke shirin ayyana ‘yancin kai.

Cibiyar yada labarai mai goyon bayan gwamnatin Sudan ta ce yau alhamis za a gudanar da bukin tube rigunan sojojin karkashin jagorancin ministan tsaro, Abdel Rahim Mohammed Hussain.

Jibi asabar ake sa ran sabuwar Jamhuriyar Kudancin Sudan zata ayyana ‘yancin kai.

Arewaci da Kudancin Sudan su na kokarin rabuwa da juna amma har yanzu akwai sauran batutuwan da ba su warware ba game da bakin iyaka da kuma yadda za a raba kudin shiga na man fetur a tsakaninsu.

A yanzu haka, sojojin Arewacin Sudan su na yakar bangarori masu goyon bayan Kudancin Sudan a Jihar Kordofan ta Kudu dake karkashin ikon Arewaci.

A halin da ake ciki, ana can ana ci gaba da shirye-shiryen bukukuwan da za a gudanar ranar asabar a Juba, babban birnin Kudancin Sudan. Hukumomi sun rufe tituna da dama ta yadda masu shirya bukukuwa zasu iya tsara irin bukukuwan da za a gudanar a ranar.