Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kuadancin Sudan Tana Haramar Ayyana 'Yancin Kai Asabar


Sojojin kudancin Sudan suka sinitir yayinda masu pareti suke gwaji a Juba.
Sojojin kudancin Sudan suka sinitir yayinda masu pareti suke gwaji a Juba.

A Juba babban birnin sabuwar kasa,a yinin yau Jumma’a baki daya masu shara da gyare-gyare suna ci gaba da aiki tukuru domin kammala shirye shiryen bukukuwa.

A Juba babban birnin sabuwar kasa,a yinin yau Jumma’a baki daya masu shara da gyare-gyare suna ci gaba da aiki tukuru domin kammala shirye shiryen bukukuwa, yayinda makada da raye raye suke rangwadawa kan titunann birnin domin ayyana ‘yancin kan kasar.

Al’umar kudancin Sudan suna kidaya sa’o’I ne kawai kamin yankin ya ayyana cin kashin kai, da manyan baki daga kasashen duniya. Duk da wadan nan bukukuwa da murna da ake yi akasin kalubale da sabuwar kasar zata fuskanta ne nan dan nan.

Kudancin Sudan din har yanzu tana ci gaba da kokarin raba kanta daga arewqaci,kuma har yanzu sassan biyu basu warware batun kan iyaka ba d a kuma rabon kudaden shiga daga mai.Sojojin daga arewacin Sudan suna gwabza fada da wasu dakaru magoya bayan kudancin Sudan,a jihar kordofan ta kudu dake karkashin ikon arewaci.

Ana sa ran yau jumma’a Mahalisar Dinkin Duniya zata kada kuri’a domin tura sojojin kiyaye zaman lafiya a kudancin Sudan, sabo da ya saukaka a yi rabuwar cikin lumana. Kudurin zai bukaci tura sojoji dubu bakwai da ‘yansanda tari tara.

Ana sa ran shugabannin kasashen Afirka 30 ciki har da shugaba Omar al-Bashir na Sudan, da babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Banki Moon, suna daga cikin wadanda zasu halarci bikin.

XS
SM
MD
LG