A yayin wannan takaddama ne gwamnatin jihar ta rarraba shagunan dake kasuwar, harma wasu daga cikin ‘yan kasuwar sun fara bada somin tabin kudaden da ake nema su biya. Sai kwatsam kwamishinan tsara biranen jihar Alhaji Hassan Baffa ya ba ‘yan kasuwar umurnin kama shagunan da suka ga dama ba tare da sun biya kudi ba.
Wannan umurni ne yasa ‘yan kasuwar komawa da cigaba da bude shaguna, sai dai ba’a kai ko’ina ba jami’an ‘yan sanda suka bayyana inda suka kori ‘yan kasuwar daga shagunan su, lamarin da ya jefa da mada cikin mawuyacin hali.
‘Yan kasuwar sun bayyana rashin jin dadinsu, domin a cewarsu kwamishina ne ya basu izinin shiga shagunan, daga baya kuma lamarin ya canza.
Yayin da ‘yan kasuwar ke ci gaba da kokawa, gwamnatin jihar ta ce bada izinin ta kwamishinan ya bada wannan umurni ba. Mr Anthony, sakataren gwamnatin jihar Taraba ya ce bada yawun gwamnatin jihar kwamishinan ya bada wannan umurni ba.
Ga rahotun Ibrahim Abdul’aziz.
Your browser doesn’t support HTML5