Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar dake Harsashen Yanayi Tace Za'a Samu Ambaliyar Ruwa a Jihohhi Ukku


Muhammadu Badaru Abubakar, gwamnan jihar Jigawa, daya daga cikin jihohin da ambaliyar ruwan zata shafa
Muhammadu Badaru Abubakar, gwamnan jihar Jigawa, daya daga cikin jihohin da ambaliyar ruwan zata shafa

Ranar Talatan nan hukumar dake harsashen yanayi tace jihohin Kano da Jigawa da Katsina da kuma Kaduna zasu samu ambaliyar ruwa a kananan hukumomi ishirin da daya.

Hukumar bada agajin gaggawa ta gargadi al'ummomin jihohin da ma wadanda suke makwaftaka dasu da suyi taka tsantsan.

Kasa da makonni biyu da suka shude ambaliyan ruwan ta lalata gonaki da gidaje da kuma rumfunan kasuwa a kananan hukumomin Kiru da Bebeji da kuma karamar hukumar Dawakin Kudu duk a jihar Kano.

Wani yace ambaliyar ruwa ta bata masa waken suya da masara da albasa da tumatiri. Suna ganin abinci ya samu sai kuma ga hasara da ta addabesu. Shi ma Sule Mogu yace ruwa da ya zo da iska sai ya cire kwanun shagonshi. Duk kayan dake ciki suka lalace.

Tuni dai jama'ar yankunan Wudil da Warawa biyu daga cikin kananan hukumomi takwas dake Kano da hukumar NEMA tayi harsashen cewa zasu samu ambaliyan ruwa suka tashi tsaye. Sun ce sun ji gargadin da hukumar tayi kuma dole ne su samu su tsira.

Wani Malam Sani Miko masanin kimiyar yanayi yayi karin haske dangane da hanyoyin da masana fannin sukan bi.. Yace mutanen suna da kayansu na gwaje-gwaje su ga menene zai iya faruwa saboda su sanarda jama'a a san irin matakan da za'a dauka..

Yace amma duk da kayan aikin da suke dashi yanayin Afirka ta Yamma gurbatacce ne. Misali iskar dake tashi daga janareto da tsoffin motoci suna tashi sama su gurbata iska. Sai a wayi gari a ga harsashen masanan bai fito fili ba, shi ya sa wani zibin sai a daukesu bazata. Wani abun ka iya faruwa ba tare da sun sani ba ko kuma ya zo bai faru ba.

Ga rahoton Mahmud Ibrahin Kwari da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG