Shugaban dai ya nada Dr Adeyemi, a matsayin mai bashi shawara akan sha’anin tattalin arziki, sai kuma Alhaji Tijjani Abdullahi, a matsayin mai bada shawar kan tsare tsare, da barrister Maryam Uwais, mai bada shawara akan raya al’umma, da kuma Sanata Babafemi, a matsayin mai bada shawara akan sha’anin siyasa.
Koda shike an yi wani dan kwaryakwaryan buki na rantsar da mutanen, wasu kwararru akan sha’anin tattalin arziki a Najeriya suna ganin da walaki wato goro a miya, domin a cewar su bai dace aba Dr Adeyemi mukamin mai bada shawara akan tattalin arzikin Najeriya ba.
Dr Muttaka Usman, shugaban sashen tattalin arziki na jami’ar Ahmadu Bello dake zaria, ya bayyana cewa Dr Adeyemi yayi aiki ne da fannin tattalin arziki na majalisar dinkin duniya, dan haka kamata yayi a ba wadanda suka san matsalar tattalin arzikin da ake fama da ita a cikin kasar ko wadanda zasu dauki shawara daga cikin kasar ba daga waje ba.
Malamin ya kara da cewa kamata yayi a sami wanda ya san tattalin arzikin kasar kamar na tsawon shekaru goma, domin a cewar sa, karanta tattalin arziki a takarda ka iya shan bam ban da yadda yake tafiya a kasa. Dan haka wanda aka dama da shi akan tattalin arzikin kasa yafi dacewa.
A waje daya wani kwararre akan sha’anin tattalin arziki Malam Shu’aibu Idris ya ce lallai akwai gyara dangane da wannan nadin da aka yi, domin abinda aka karanta da kwarewa a karatu daban yake da abinda ake iya aiwatarwa ko aka sani a zahiri.
Ga rahoton Umar Faruk Musa.