A jiya ne kwamandan riko na rundunar sojin shiyya ta bakwai dake garin Maiduguri jihar Borno, Burgediya Victor Ezokwu ya kaddamar da wannan kotu a garin Maiduguri, inda ya bayyana cewa yanzu haka akwai mutane guda ashirin da suke gaban wannan kotu.
Kwamandan ya bayyana cewa yau za’a yankewa jami’an hukunci bisa samun su da laifuka daban daban a yayin da suke gudanar da ayyukan su kamar sayar da makamai, da sauran laifuka da suka sabama dokokin aikin soja a lokacin da jami’an ke fafatawa da ‘ya’yan kungiyar boko haram a gabas maso arewacin kasar.
Ya kara da cewa sun gayyaci ‘yan jarida da lauyoyi ne domin su nunawa duniya cewar ba a boye suke gudanar da ayyukansu ba, kuma dole ne su gudanar da ayyukan nasu cikin kwarewa, dan haka dole ne a hukunta duk wanda ya aikata laifi dai dai da irin laifin da ya aikata.
Sojoji ashirinne zasu fuskanci shari’ar, kuma goma sha shidda daga cikin su kananan jami’ai ne, sauran hudun kuma manyan jami’an soja ne, kuma kowanensu zai fuskanci shari’a bisa irin laifin da ya aikata.
An gurfanar da dukkan jami’an cikin kayansu na sarki dauke da mukamansu, sai dai basu da huluna a kawunansu.
Wannan kotun dai ita ce ta farko da aka kafa a jihar, wadda zata hukunta duk wani jami’in sojin da aka kama da aikata ba daidai ba a lokacin da yake gudanar da ayyukansa a arewa maso gabashin kasar. Burgediya janar Adeniyi, ne shugaban kotun kuma ya tambayi jami’an da aka gurfanar ko suna da wani ja akan tuhumar da ake masu, amma babu wanda ya amsa.
Ga rahoton Haruna Dauda Biu.