Shugaban babbar jami’iyar adawan kasar ta Cameroon Renaissance Movement, (MRC), Maurice Kamto ne ya kira wannan zanga zanga a ranar 22 ga watan Satumba 2020, domin nuna rashin amincewa da wasu shawarwarin da gwamnati ke dauka a kan zabukan yanki.
A ranar 15 ga watan Satumba ne ministan sadarwa ya yi wa jam'iyun siyasa kashedi cewa duk wanda ya gudanar da zanga zanga za a dauke shi a matsayin masu tada kayar baya, a dan haka duk wanda ya gudanar da zanga zanga fadin kasar, zai fuskancin jan kunne karkashin dokar yaki da ayyukan ta’addanci.
Wani dan rajin kare hakkin bil Adama kuma darektan kugiyar Human Rights Watch a Afrika ta Tsakiya, Lewis Mudge, ya ce wannan mataki ne da gwamnatin Kamaru ke dauka na take ‘yancin gudanar da taro ta hanyar amfani da muguwar dokar yaki da ta’addanci. Ya ce ya kamata hukumomin Kamaru su kare hakkin ‘yan kasa wurin gudanar da taro amma ba su hana ba.
Jami’an tsaro sun kai samame a gidan madugun ‘yan adawan Maurice Kamto kana suka yi awan gaba da shi lamarin da ya hana shugaban ‘yan adawan shiga wannan zanga zangar day a kira. Haka zalika aka kama mabobin jami’iyar adawa ta MRC da dama.
A wata sanarwa da gwamnatin Kamaru ta fitar da yammacin ranar Litinin kafin zanga zangar, mai Magana da yawun gwamnati Rene Emmanuel Sadi ya ce wannan zanga zangar wani yunkuri ne na bijirewa hukumomi da kuma take dokar zaman lafiyar jama’a.
Shugaba Biya dai ya kwashe shekaru 39 yana mulkin kasar Kamaru. An sake zaben Paul Biya ne a shekarar 2018 a wani sabon wa’adi na shekaru bakwai nan gaba. Kasar Kamaru tana fama da rigingimun ‘yan aware da ‘yan tawayen Bangi da kuma ‘yan ta’addan Boko Haram.
Ga rahoton Mohammed Awal Garba daga Kamaru:
Your browser doesn’t support HTML5