Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Madugun 'Yan Adawa a Ivory Coast Ya Bukaci Jama'a Su Kauracewa Zaben Kasar


Dan takarar babbar jam’iyyar adawa a Ivory Coast ya bukaci jama’a su kauracewa zaben kasar don hana sake zaben Shugaba Alassane Outtara yin wa’adi na uku a wata mai zuwa.

Henri Konan Bedie ya yi wannan kiran ne a ranar Lahadi 20 ga watan Satumba a Abidjan babban birnin kasar, a lokacin wani taro tare da sauran ‘yan takara daga jam’iyyun adawa da magoya bayansu.

Kasar ta yammacin Afirka da ke fuskantar tashin hankali, akalla mutane goma sha biyu aka kashe tun daga watan jiya, bayan da Outtara dan shekaru 78 ya karya alkawarin da ya yi a farkon wannan shekarar na cewa ba zai sake neman takara ba.

Outtara ya sauya matsayinsa kuma a hukumace ya amince da zaben da jam’iyyarsa mai mulki ta yi masa na sake tsayawa takara bayan da wanda aka zaba ya maye gurbin, Firayim Minista Amadou Gon Coulibaly ya mutu kwatsam sakamakon bugun zuciya a watan Yuli.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG