Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Khalifa Haftar Zai Bari a Fara Aikin Man Fetur a Libya


Filin hakar man fetur na El Sharara a Libya
Filin hakar man fetur na El Sharara a Libya

Kwamandan dakarun Libya da ke rike da yankin gabashin kasar Libya, Khalifa Haftar ya ce zai bari a ci gaba da aikin sarrafa danyan man fetur bayan da aka kwashe wata takwas da dakatar da ayyukan. Haftar ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a kamar yadda kamfanin dillancin labaran Reuters ya ruwaito.

Wani babban dan siyasa a Tripoli babban birnin kasar, ya ce za a kafa wani kwamiti wanda zai sa ido wajen ganin an yi raba daidai na kudaden da aka samu daga arzikin man kasar.

Sai dai kamfanin da ke sarrafa man fetur din kasar ta Libya, ya ce ba zai yi hanzarin dage matakan da ya saka na fitar da man kasar zuwa kasashen waje ba har sai an akwar da mataakn sojin da aka saka a wuraren sarrafa man.

Rufe ayyukan mai da sarrafa mai da dakarun suka yi, ya sa Libya ta yi asarar dala biliyan 9 a wannan shekara kamar yadda babban bankin kasar ya fada a wannan mako.

Matakin ya kuma haifar da cikas a kokarin da ake yin a samar da masalaha ga rikicin siyasar kasar bayan wani farmaki da Haftar ya kai a Tripoli a watan Yuni.

Kasar ta Libya ta shiga rudanin siyasa ne bayan da aka hambarar da gwammatin tsohon shugaban kasar Moamar Ghadafi a watan Oktoban 2011.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG