A yayin da jamhuriyar Nijer ke shugabancin Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a watan nan na Satumba da muke ciki, hukumomin kasar sun shirya wani taron mahawara domin gabatar da wasu mahimman ayyukan da Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar a kasashe daban daban da nufin wanzar da zaman lafiya.
Tun a ranar 1 ga watan Satumban da muke ciki ne jamhuriyar Nijer ta dare kujerar shugabancin karba-karbar Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya sabili kenan da hukumomin kasar ke amfani da wannan dama domin kara wayar da kan jama’a a game da rawar da Nijer ke takawa a ayyukan wanzar da zaman lafiya karkashin inuwar Majalisar Dinkin Duniya. Commandant Ali Ibrahim na daga cikin shika shikan wannan zama kuma ya bayyana rawar da Nijer ke takawa wajen warware matsalolin yankin Sahel, wanda don haka ta ke tasiri a harkokin Kwamitin Sulhun na Majalisar Dinkin Duniya.
Daga farkon karbar ragamar Kwamitin Sulhu kawo yau Nijer ta sami nasarori sosai akan maganar warware bakin zaren da ke sarkewa a tsakanin mambobin kwamitin sulhu kuma kasar za ta ci gaba da bullo da sabbin shawarwari har I zuwa ranar da za ta sauka daga wannan mukami, wato 30 ga watan satumba inji ministan harakokin wajen kasar Kalla Hankouaro.
Gwamnatin ta Nijer na alfahari da gudunmowar ‘yan kasar farar hula da jami’an tsaro don ganin Majalisar Dinkin Duniya ta cimma gurin da ta sa gaba.
A ci gaba da raya watan shugabancin na Kwamitin Sulhu na MDD, an shirya wani baje kolin hotuna da zummar karrama sakatarori da manyan jakadun da suka jagoranci Majalisar Dinkin Duniya daga kafuwarta kawo yau. Pr Tidjani Alou ne ya yi gabatarwa a madadin kwamitin tsare tsaren wannan buki.
Taron raya watan shugabancin na Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai ci gaba da wata mahawara akan illolin canjin yanayi da za a gudanar a Yamai da nufin nazarin hanyoyin da za a bullo wa wannan kalubale da ya sha gaban duniya. a ranar 1 ga watan Janairun da ya gabata ne Nijer ta haye kujerar Kwamitin Sulhu a matsayin mai wakilcin wucin gadi, bayan la’akari da mahimancinta akan sha’anin tsaro a yau a yankin sahel.
Ga Sule Barma da cikakken rahoton cikin sauti:
Facebook Forum