'Yan Kabilar Igbo Mazauna Jihar Naija Sun Yi Watsi Da Yunkurin Kafa Biafra

Wasu masu gwagwarmayar kafa kasar Biafra a Najeriya yayin wani gangami da suka yi

‘Yan kabilar Igbo dake zaune a jihar Naijan Najeriya, sun bi sahun takwarorinsu dake zaune a wasu yankunan Arewacin kasar wajen yin watsi da gwagwarmayar da wasu ‘yan kabilar su ke yi ta neman kafa kasar Biafra.

‘Yan kabilar Igbo dake zaune a Jihar Naija Sun yi watsi da yunkurin neman kafa Kasar Biafra a wani gangami da suka gudanar a gidan gwamnatin jihar Naijan dake Minna, babban birnin jihar.

“Mun matsu mu ji kalamanka akan wa’adin da wasu matasan arewacin kasar nan suka ba mu na mu koma yankin da muka fito, bukatarmu ita ce mu samu tabbacin cewa bama cikin hadari.” In ji shugaban ‘yan kabilar ta Igbo a jihar Cif Eze, yayin da yake jawabi a lokacin gangamin.

Sai dai gwamnan jihar ta Naija, Alhaji Abubakar Sani Bello, ya ce ‘yan kabilar ta Igbo su kwantar da hankalinsu su ci gaba da harkokinsu domin babu abinda zai same su.

“Wannan rigima ko rikici da ya dan taso za a yi maganin shi, kuma ina tabbatar masu mu nan a jihar Naija babu wani abu da zai samu wani Igbo, su ci gaba da kasuwancinsu.” In ji gwamna Bello.

A makwannin bayan ne wata kungiyar matasan arewa ta bai wa ‘yan kabilar ta Igbo wa’adi zuwa watan Oktoba da su tattara inasu-inasu su bar yankin arewacin Najeriya su koma yankinsu.

Wannan wa’adi martani ne ga kiraye-kirayen da kungiyar mai gwagwarmayar ganin an kafa Biafra IPOB ke yi na cewa a raba kasar, a karkashin jagorancin Nnamdi Kanu, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce.

Saurari cikakken rahoton Mustapha Nasiru Batsari daga Minna:

Your browser doesn’t support HTML5

‘Yan Kabilar Igbo Mazauna Jihar Naija Sun Yi Watsi Da Yunkurin Kafa Biafra - 1'57"