Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manjo Janar Irabor Yace Rashin Kula da Iyakokin Kasashen Tafkin Chadi Na Yiwa Tsaro Barazana


Manjo Janar Leo Irabor
Manjo Janar Leo Irabor

Yadda iyakokin kasashen tafkin Chadi dake fada da kungiyar Boko Haram suke wayau babu kariya na yiwa harkokin tsaro barana inji Manjo Janar Lucky Irabor kwamandan rundunar hadin gwuiwa dake yaki da 'ayan Boko Haram a kasashen Najeriya, Chadi,Kamaru da Nijar.

Manjo Janar Leo Irabor ya bayyana yadda iyakokin kasashen tafkin Chadi ke nan sakaka ka iya kawowa harkokin tsaron kasashen barazana.

Yace a fafutikar da ake yi da 'yan Boko Haram idan aka yi la'akari da iyakokin Chadi, Kamaru, Nijar da Najeriya abun damuwa ne. Chadi ita ce ta fi yawan iyakoki sai kuma Nijar wadda ita ce ta biyu. Kasashen biyu basu da yawan jama'a, ke nan akwai yankunansu da babu kowa ciki.

Yace idan ba'a damu da abubuwan dake faruwa a kasashen dake makwaftaka da Najeriya ba duk abun da ya faru a kasashen ka iya yin tasiri a Najeriya saboda "mun san albarkatun da muke dashi a kasarmu", inji Janar Irabor.

Akwai yiwuwar wasu su yi anfani da kasashen dake makwaftaka da mu su haddasa rigima domin cin moriyar albarkatunmu wannan wani abun da yakamata mu yi la'akari dashi a tsarin tsaronmu acewar Janar Irabor.

Janar Irabor ya kara da cewa akwai karancin tsaro akan iyakokin Najeriya. Yace idan an duba matsayin Najeriya a yankin tafkin Chadi iyakokin kasar na nan sasarai, wayau a bude babu wani sha'anin tsaro. Yana ganin hakan ka iya sa kowa ma ya kutsa cikin kasar musamman daga shiyar arewa maso gabas.

Tsohon sakataren raya tafkin Chadi Dan Masanin Fika yace kalamun Janar Irabor na kan hanya. Yana mai cewa cikin jihohin Najeriya 36 jihar Borno ce kadai take makwaftaka da kasashe uku dalili ke nan da kayan yaki iri iri suke shiga jihar.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG