Akalla mutane 6,000 da shanunsu da dama sun shiga mawuyacin hali yayin da suke tserewa rikicin jihar Taraba da ake fama da shi a yankin Mambila dake arewa maso gabashin Najeriya.
‘Yan gudun hijrar suna neman mafaka ne a kauyukan dake kan iyakar kasar ta Najeriya da makwabciyarta Kamaru, inda rahotanni suka nuna cewa da yawa daga cikinsu sun mutu.
Wakilin Muryar Amurka a Kamaru, Moki Edwin Kendzeka, ya ruwaito cewa hukumomin lafiya a kasar ta na yekuwar neman a kawo wa mutanen da suka tsira dauki, musamman a wani kauye da ake kira Atta wanda ke dauke da ‘yan gudun hijira kusan 4,000.
Hukumomin lafiya a wannan yanki sun bayyanawa Muryar Amurka cewa mafi yawan wadanda ke gudun hijirar, mata ne da kananan yara.
Wakilin Muryar Amurka a yankin Taraba da Adamawa, Ibrahim Abdulaziz, ya tattauna da Sanata Yusuf Aliyu Yusuf, dake wakiltar yankin da ‘yan gudun hijirar suka fito daga Najeriya, wanda ya yi mai karin haske kan halin da ‘yan gudun hijrar ke ciki da kuma kiran da ya yi na a kai masu dauki.
Saurari yadda tattaunawarsu ta kaya:
Facebook Forum