Gwamnan Jihar Neja Alh.Abubakar Sani Bello, yayi wata ganawa ta musamman da Tsoffin Gwamnoni yan asalin jihar dama tsaffin Mataimakan Gwamnonin da kuma Tsoffin Ministoci yan asalin Jihar domin neman bakin zaren akan matsalolin da suka addabi Jihar.
Bayanai sun nuna cewar ganawar nada nasaba da matsalolin da jihar ke fama da su iri iri, kama daga matsalar tattalin arziki da takun sakar dake tsakanin jihar Niger da gwamnatin taraiya akan wasu filaye da jihar ke zargin cewa gwamnatin taraiya ta karbe mata. Sai kuma matsalar tsaro daya adabi wasu sassa na jihar.
Daga cikin tsafin gwamnonin da suka yi ganawar da gwamnan harda wanda ya gada Dr Muazu Babangida Aliyu.
Tsohon gwamnan jihar Katsina Kanal John Yahaya Madaki mai ritaya, shie ya yiwa yan jarida bayanin gudanar da wannan taro. Kanal Madaki yace sun tattauna akan tattalin arziki da kuma wasu yankunan ko kuma filaye da gwamnatin tarayar ta karbe. Da kuma matakin da jihar zata dauka, ko kuma ta yi domi a mayar mata da filayen.
Haka kuma Kanal Madaki yace sun tattauna kan matsalar tsaro. Ya kuma ce sauran batutuwan kuma, kwamitin da aka kafa shi zai yi su.
Facebook Forum