A cewarsu dan takararsu Mahaman Ousmane ne ya lashe zaben 21 ga watan fabrerun 2021.
Wannan Gangami dake matsayin na farko da jam’iyun hamayyar ke shiryawa tun bayan da Mohamed Bazoum ya yi rantsuwar kama aiki a ranar 2 ga watan Afrilun 2021 wani yunkuri ne na sake jaddadawa jama’a cewa adawa na nan daram akan matsayinta.
Hasalima jam’iyun na CAP 20 21 da ACC da FRC na akan bakansu na masu ja game da sakamakon da ya bayyana dan takarar PNDS a matsayin wanda ya ci zaben da ya gabata kamar yadda kakakinsu Habibou Kane Kadaoure ya shaida wa Muryar Amurka.
Ya kuma kara da cewa sun kai kara kotun ECOWAS saboda abokansu da aka tsare bayan sakamakon zagaye na biyu na neman shugaban kasa.
A ci gaban wannan sanarwar Jam’iyun na hamayya sun bayyana yadda suke kallon kamun ludayin Mohamed Bazoum a tsawon kwanaki 100 na shugabancin kasa.
Zakari Aliyu, sakataren jam’iyar RDR Canji ta Alhaji Mahaman Ousman ya ce har yanzu akwai matsallar tsaro a dukkan fadin kasar duk da cewa gwamnati na nuna da samun nasarar magance matsalolin kasar.
Amma da yake maida martani game da wadannan korafe-korafe wani na hannun daman shugaban kasa Alhaji Mai Boucar kusa a jam’iyar PNDS Tarayya ya ce maganganu ne irin na wanda ya rasa tudun dafawa.
Wani abin da manema labarai muka lura da shi shi ne, shugabanin jam’iyar Moden Lumana ta ‘yan hamayya ba su halarci wannan gangami ba.
Wani jigonta Bana Ibrahim na hannun daman tsohon fira minista Hama Amadou ya rubuta a shafinsa na facebook cewa lokacin fitar da wannan sanarwa bai yi ba amma kuma ya jaddada cewa jam’iyyar na nan a matsayinta na mai adawa da manufofin gwamnatin Jamhuriya ta 7.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5