Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dokokin Nijer Ta Fara Taron Nazarin Wasu Sauye Sauyen Kasafin Kudin 2021


Majalisar dokokin jamhuriyar Nijer ta fara gudanar da taron gaugawa bayan da gwamnatin kasar ta bukaci a aiwatar da gyaran fuskar kasafin kudaden 2021 sakamakon sauye sauyen da gwamnatin shugaba Mohamed Bazoum ta zo da su.

Matakin takaita yawan membobin gwamnati wanda shugaban kasar Nijer ya dauka bayan da ya karbi ragamar mulki a ranar 2 ga watan Afrilun da ya gabata da a daya gefe wasu bukatun da gwamnatin tace sun karu akan wadanda ke kunshe a kasafin shekarar nan ta 2021 ne ya sa majalisar soma wannan zaman domin tantauna wannan bukata ta kwaskware kasafin kudin kasa.

Ganin yadda gwamnatin ta bukaci majalisa ta bata izinin kara yawan kudade akan wadanda kasafin ya kunsa a can farko ya sa bangaren adawa jan hankulan ‘yan majalisar su maida hankali don tabbatarwa kansu an yi abin don talakka inji Honorable Ibrahim Yacouba.

To amma a cewar honorable Boukari Sani Zilly na bangaren masu rinjaye bukatun tallaka ne mafarin bullo da wannan gyaran fuskar.

Gwamnatin da ta shude ce ta tsara kasafin kudin shekarar 2021 wanda kuma majalisar dokoki ta wancan lokaci ta yi na’am da shi a wani lokacin da dukkansu ke gab da kammala wa’adinsu.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00

XS
SM
MD
LG