A Jamhuriyar Nijar ‘yan hamayya sun bayyana rashin gamsuwa da kamun ludayin shugaba Mohamed Bazoum shekara 1 da darewarsa kan karagar mulkin kasa.
Da yake bayyana matsayinsa dangane da yadda shugaba Mohamed Bazoum ya tafiyar da al’amura a tsawon watanni 12 na farkon wa’adin mulkinsa, Alhaji Doudou Rahama, jigo a jam’iyar RDR Canji ta tsohon shugaban kasa Mahaman Ousman bugo da kari dan takara a zagaye na 2 na zaben shugaban kasa, ya ce, su ‘yan hamayya ba su ga wani sauyin da aka samu ba.
A bangaren yaki da cin hanci ma Doudou Rahama ya ce a na nan gidan jiya domin har i zuwa yau babu wani hobbasa na zahiri da aka yi a wannan fanni.
A makwannin farkon darewarsa kujerar shugabancin kasa Mohamed Bazoum ya gana da shugabanin kungiyoyi da na rukunonin al’uma daban-daban in ban da ‘yan adawa dalili kenan a hirarmu da shi a albarkacin cika shekara daya da samun wannan matsayi muka tambaye shi me ya sa bai gana da shugabanin jam’iyun hamayya ba?
"Suna cewa, ni ba zabbaben shugaban kasa ba ne, in har na ce zan yi murabus don su hau mulki, to abun bai da ma'ana, in za su min tambayoyin da ba ni da maganinsu, to babu amfanin mu ga juna, amma ran da na ga akwai alama mu gana kuma wannan ganawar ya yi tasiri, to za mu yi shi."
A yanzu haka jam’iyyun da suka goyi bayan takarar Mahamane Ousman a fafatawarsa da Mohamed Bazoum na PNDS Tarayya na jiran zuwa ranar 31 ga watan mayun gobe inda ake sa ran kotun ECOWAS za ta bayyana hukunci bayan da Mahaman Ousaman ya shigar da kara ya na mai kalubalantar sakamakon da ya ayyana shi matsayin wanda ya sha kaye a zaben na ranar 21 ga watan fabrerun 2021.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5