Yan gwaggwarmayar kare hakin bil'adama sun ce a kanshe sama da mutane tamanin a tarzomar kin jinin gwamnati ta baya bayan nan

Masu zangar kasar Siriya suna raira taken kin jinin shugaba Bashar al-Assad

Wata kungiyar rajin kare hakkin bil'adama ta ce jami’an tsaro a Syria sun hallaka sama da mutane 80 cikin sa’o’i 24 da su ka gabata, wanda hakan ya sa ya zama daya daga cikin lokutan da aka fi kashe-kashe a tsawon watanni 8 da aka yi ana bore wa shugaba Bashar al-Assad.

Wata kungiyar rajin kare hakkin bil'adama ta ce jami’an tsaro a Syria sun hallaka sama da mutane tamanin cikin sa’o’i ishirin da hudu da suka gabata, wanda hakan ya sa ya zama daya daga cikin lokutan da aka fi kashe-kashe a tsawon watanni 8 da aka yi ana bore wa shugaba Bashar al-Assad.

Kungiyar mai hedikwata a Burtaniya da ke sa ido kan al’amuran hakkokin bil’adama a Syria, ta gayawa Muryar Amurka a jiya Talata cewa ta tattara bayanai game da kisan fararen hula talatin da takwas da wadansu sojoji goma sha takwas da suka balle a lardin Daraa ran Litini. Kungiyar ta kuma bayar da rahotannin mace-mace a biranen Hama da Homs da ke yankin tsakiyar kasar, ciki har da mutane da dama da aka sami gawarwakinsu da alamomin gallazawa.

Kungiyar ta ce dakarun Syria masu zaman kansu da suka hada da sojojin da suka canza sheka sun kashe sojojin gwamnati akalla talatian da hudu a wata fafatawar da aka yi ranar Litini.

Ba a iya tabbatar da wannan addadi na wadanda abin ya rutsa da su ba saboda Syria ta haramtawa akasarin ‘yan jaridan kasashen waje shiga cikin kasar. ‘Yan rajin kare hakkin bil'adama na Syria suka ce an hallaka kimanin mutane 200 a wannan watan a yayin da gwamnati ke kokarin murkushe masu zanga zanga.

A halin da ake ciki kuma tsohon shugaban hukumar leken asirin Saudiyya kuma tsohon Jakadanta a Amurka, Yarima Turki al-Faisal, yace babu ko tamtama tilas ne shugaban Syria ya sauka daga mulki a daidai lokacin da kiraye kirayensa na ya daina daukar tsauraran matakan murkushe ‘yan tawaye ke ta karuwa.

Turki, wanda yayi magana da manema labarai a birnin Washington, yace Mr. Assad bai saurari kiraye kirayen ya daina kuntatawa masu zanga-zangar kyamar manufofin gwamnati ba, saboda haka, a ganinsa, ya kamata ya sauka.