Wata kungiyar kare hakkin Bil-Adama a Syria ta ce jami’an tsaron Syria sun kashe fiyeda mutane 80 cikin sa’o’I 24 da suka wuce, hakan ya sa wunin jiya litinin ya kasance mafi muni tun fara bore kan mulkin shugaba Assad da ahalin yanzu ya kai wata takwas.
Kungiyar kare hakkin Bil-Adama ta Syria mai cibiya a Ingila, ta gayawa Muriyar Amurka talata cewa tana da bayanai da suka nuna an kashe farar hula 38, da wasu 18 da ake zargin sojoji ne da suka sake sheka a lardin Daraa, a jiya litinin. Haka kuma kungiyar ta fada cewa an kashe mutane masu yawa a Hama da kuma Homs a jiya litinin, wadansu daga cikinsu an ga gawarwakinsu a kan titi d a alamun an gana musu azaba.
Kungiyar ta bada rahoton rundunar ‘yan tawayen kasar da ta hada sojoji d a suka sake sheka ta bada labarin kashe sojojin gwamnati 34 a wani fada da suka gwabza jiya litinin.
Babu wata kafa mai zaman kanta wacce ta gaskanta yawan mutane da aka kashe domin Syria ta hana galibin ‘Yan Jarida daga kasashen ketare aiki cikin kasar. Kungiyar rajin kare hakkin Bil-Adama ta kasar tace kimanin mutane metan ne aka kashe cikin watan nan a yunkurin gwamnatin shugaba Bashar al-Assad na murkushe ‘yan tawaye galibinsu a lardin Homs.