A wani sabon yunkuri ta fuskar difilomasiyyan shugaban Amurka Barack Obama zai tura sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton ta kai ziyara kasar Burma cikin watan gobe
Ziyarar da Clinton zata kai Burma itace ta farko cikin shekaru 50 ga babban jami’in Amurka mai wan nan mukamin zuwa kasar wacce ta kasance saniyar ware.
Mr. Obama ya bayyana hakane a tsibirin Bali na Indonesia, shugaban yace Amurka tana maida martani ne kan “alamun ci gaba” data gani daga gwamnatin ta Burma wacce har yanzu soja ke da ikon fada aji.
Mr. Obama ya bada misali da matakan da gwamnatin kasar ta dauka na fara shawarwari da shugabar ‘yan hamayya Aung San Suu kyi, sakin wasu fursinonin siyasa, da a kuma sakarwa ‘yan siyasa mara.
Shugaba Obam yace yayi magana da shugabar ‘yan hamayyar Aung San Suu kyi ta woyar tarho, kuma tana goyon bayan Amurka ta tsoma baki domin a samu ci gaba.
Shugaban na Amurka yace a lokacin ziyarar sakatariya Clinton zata duba hanyoyin da Amurka zata taimaka a samu ci gaba a aiwatar da sauye sauyen siyasa, mutunta hakkin Bil-Adama,d a kuma sulhu.Sakatariya Clinton zata yi tattaki ne ranar daya zuwa biyu ga watan Disemba.
Ahalin yanzu kuma shugaban na Amurka ya gana da wasu shugabannin kasashe dake Asiya dake halartar taron kolin kungiysar raya tattalin arzikin yankin da ake yi a tsibirin Bali dake Indonesia.
Shugaban ya fara ganawar ce da shugaban India Manmoha Singh.