Hukumomin kasar Amurka sun bankado wata babbar hanyar karkashin kasa ta yin fasa kwaurin kwaya a kan iyakar Amura da Mexico, sannan suka kama tabar wiwi mai nauyin ton goma sha hudu, sun yi wannan nasara ce a lokacin wasu tone-tone masu nasaba da wani binciken da ake yi.
Jami'ai sunce hanyar karkashin kasar ta kan iyaka ta yi tsawon kimanin mita 400 kuma ta hadu da wasu manyan gidajen ajiya a Tijuana kasar Mexico da kuma wata cibiyar masana'antu a San Diego, a yankin California. Jami'an da ke bincike sunce haka kuma a cikin hanyar karkashin kasar da aka gano ranar Talata, an kakkafa pila kuma akwai wutar lantarki da kuma 'yan kafofin shiga da fitar iska. Rundunar jami'an tsaron hadin guiwa ta musamman ta San Diego itace ke gudanar da binciken.
A cikin watan Nuwamban shekarar da ta gabata ma, an kai wasu samamen ba zata kan wasu hanyoyin karkashin kasa guda biyu da suka hada California da Mexico, a wancan lokaci ma an kama tabar wiwi mai nauyin ton hamsin a bangarorin kan iyakar biyu. Su ma a cikin su akwai layin dogo, da wutar lantarki da kuma kafofin shigar iska da fitarta. Hanyoyin karkashin kasar na daga cikin dimbin irin su da aka bankado a 'yan shekarun nan.
Yanzu haka ana fama da mummunan tashin hankalin kungiyoyin 'yan banga masu dillancin kwaya, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutanen kimanin dubu arba'in da biyar kamar yadda kiyasi ya nuna, hakan kuwa tunda shugaba Felipe Calderon ya kama mulki a karshen shekarar dubu biyu da shida kuma ya fara daukan matakan nuna ba sani ba sabo ga kungiyoyin dillalan kwaya.