'Yan Gudun Hijirar Somaliya Sun Yi Murnar Dawo Da Su Gida

  • Ibrahim Garba

Wasu 'yan kasar Somaliya

Dama an ce kowa ya bar gida, gida ya bar shi. Wasu 'yan gudun hijarar kasar Somaliya da aka dawo da su gida daga kasar Libiya, sun tabbar da hakan ta wajen gode ma Allah da aka maida da su kasarsu ta haihuwa.

Cikin matukar doki aka dawo da wasu ‘yan gudun hijirar Somaliya su wajen 12 daga kasar Libiya jiya Asabar.

Wasunsu sun durkusa kan guyawunsu sun a ta kuka; wasunsu kuma na ta ruku’u da sujjada; a yayin da wasu ke ta raira taken kasarsu ta Somaliya a yayin da su ke saukowa daga jirgin saman kasar Turkiyya da ya dauko su daga kasar Libiya, inda wasunsu su ka makale na tsawon shekaru da dama.

Tun daga 2014 kasar Libiya ta zama wani zango na ‘yan gudun hijira daga Afirka da Gabas Ta Tsakiya wadanda ke kokarin guje ma rashin kwanciyar hankali zuwa nahiyar Turai.