Banda rashin abun yi basu da ingantacen muhalli suna cunkushe a wuri guda idan kuma wasunsu sun kamu da rashin lafiya basu da kudin sayen magani.
Wata malama da take da cikin wata takwas yayinda 'yan Boko Haram suka kai masu hari dole ta haihu ba tare da samun kula ba. Yanzu inda suke da maigidanta da 'ya'ya babu kudin sayen magani. Ta bukaci a yi mata taimako tare da diyarta su samu magani.
A jihar Kano akwai 'yan gudun hijira kimanin dubu goma dake samun mafaka a unguwanni daban daban a birnin Kano da kewaye. 'Yan gudun hijiran da suka samu kubuta daga hannun 'yan Boko Haram sun fito ne daga Bama da Gwozah da Gamboru Ngala da wasu sansan jihar Borno.
Galibinsu hukumomin Hisbah da ta bada agajin gaggawa na jihar Kano ke taimaka masu wajen samun matsuguni da jagorancin samun tallafi daga daidaikun mutane da kungiyoyi.
Malama Zara Umar mataimakiyar kwamandan hukumar Hisbah mai kula da bangaren mata tace suna da rajistan gidajen da 'yan gudun hijiran suke zaune. Wasu da garuruwansu nada gidaje sun koma wadanda kuma babu gidaje a nasu suna nan a Kano. Ana dan tallafa masu. Yawancinsu basu da maza saboda ko an kashesu ko kuma sun yi wajen Kamaru.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5