Kama daga Patiskum da Goza da Biu da Gombe har zuwa Mubi, wadanda a baya suka fada hannun mayakan Boko Haram yanzu za a iya cewa hankula sun kwanta inda har an bude makarantu da sauran guraren hada hadar jama’a, ta yanda jama’a ke ci gaba da gudanar da rayuwarsu cikin tsanaki da kwanciyar hankali.
Abdullahi Ahmed Baza, dan asalin yankin Michica ne wanda yayi wa wakilin Muryar Amurka Ibrahim Abdul’aziz bayanin cewa an samu nasara da zaman lafiya a yakin, mutanen da suka fice yanzu duk sun dawo, duk da dai suna cikin halin neman taimako amma akwai kwanciyar hankali yanzu.
Baya ga harkokin kasuwanci da kuma zamantakewa yanzu haka an bude makarantu inda lamura suka fara komawa dai dai. Safiya Yaya Saleh, wata dalibace a Jami’ar jihar Adamawa dake garin Mubi, ta tabbatar da cewa yanzu kan komai ya fara dawowa yadda ya kamata.
A baya shugaban Najeriya Mohammadu Buhari, ya daukarwa dakarun sojan kasar wa’adin watan Disambar da ta gabata da su kawo karshen Boko Haram, batun da shugaban ke ganin kwalliya na biyan kudin sabulu a yanzu. Koma me ake cikin yanzu fatan talakan Najeriya shine lamurra su koma dai dai.
Domin karin bayani.