Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nasarorin Da Rundunar Zaman Lafiya Suka Samu Kan Boko Haram


Sojojin shiyya ta 7 dake Maiduguri sun gano inda harhada bam a Kumshe
Sojojin shiyya ta 7 dake Maiduguri sun gano inda harhada bam a Kumshe

Rundunar sojan Najeriya shiyya ta bakwai dake garin Maiduguri tace ta samu nasarar kawar da wani harin wasu yan kungiyar kunar bakin wake mata 4 da ake kyautata tsammanin sun fito ne daga dajin Sambisa, kuma sun tunkari wani kauye da ake kira JImini Bolori.

An kuma samu nasarar kame wasu mata guda biyu da ake zargin cewa suma yan kunar bakin wake ne dake tunkarar kauyen Madiyari. Kwamandan rundunar sojan da ake kira Operation Lafiya Dole, Janar Lucky Irabor, ne ya shaidawa manema labarai cewa rundunar ta su na ci gaba da samun nasarori game da yaki da yan ta’adda da suka sa gaba.

Ya kuma kara da cewa sun gano inda ake horas da yan ta’addar a wani kauye da ake kira Madalla dake karamar hukumar Dikko a jihar Borno. Yace sun sami nasarar kashe daya daga cikin shugabannin kungiyar da ake kira Amir da kuma wasu guda 6 sannan sun kama wasu guda 5 a raye, har ma sun lalata wasu motoci guda biyar na ‘yan kungiyar Boko Haram.

Rundunar sojan tace ta samu nasarar kubutar da wasu mutane dubu 1 da ‘yan ta’addar sukayi garkuwa da su, haka kuma rundunar Lafiya Dole ta gano inda Boko Haram ke sarrafa boma bomai a wasu kauyuka da suka hada da Boboshe da Garna Kyari da Gimba da Ajari dukkansu a karamar hukumar Bama, sun kuma gano wasu tukwanen iskar gas guda 8 da ake amfani da su wajen kera boma bomai a wata makarantar firamare.

A ranar 28 ga watan Afrilu ne rundunar ta gudanar da wani sintiri a kauyen Bogoro da Dugunu, bayan da suka isa kauyen Baraka suka ci karo da wasu ya yan kungiyar Boko Haram, inda suka sami nasarar kawar da su, har suka ci gaba da nausawa zuwa yankin Jidda village inda anan ma suka kara arangama da wasu yan kungiyar Boko Haram har suka kashe mutane 4.

Daga karshe rundunar ta gano wani makeken rami da yan Boko Haram ke jefa mutanensu da suka mutu, haka kuma sun gano wasu bindigogi kirar AK47 da alburusai masu yawan gaske, sai kuma wani dakin ajiye kayan abinci da na magunguna harma da kwayoyin bugarwa wanda ake zargin sune ake baiwa mutanen dake zuwa suyi kunar bakin wake. Kwamandan rundunar Lafiya Dole, yace lokacin da suke gudanar da wannan aiki soja daya daga cikin jami’an soja ya sami raunin harbin bindiga wanda yanzu haka ke karbar magani.

Domin karin Bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG