Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Gudun Hijira Sun Yaba Ma Shugaba Buhari


Wasu 'yan gudun hijira na karbar tallafi
Wasu 'yan gudun hijira na karbar tallafi

Shugaba Buhari na cigaba da samun yabo daga wadanda su ka san bala'in Boko Haram, musamman 'yan gudun hijira.

‘Yan gudun hijira da ke sansanonin Malkohi da Damare da ke jahar Adamawa sun ce mulkin canji na Shugaba Muhammadu Buhari ya kyautata halin rayuwarsu, shekara daya bayan ya amshi madafun mulki.

Wannan bayanin na kunshe a hirarrakin da wakilinmu Sanusi Adamu ya yi da ‘yan gudun hijirar, a lokacin da ya ziyarci sansanonin domin ya yi nazarin ko an samu sauyi a yanayin rayuwarsu yanzu da Shugaba Buhari ke gab da cika shekara guda akan karagar mulkin Najeriya.

Mal. Modu Gana shugaban ‘yan gudun hijira na sansanin Damare, wanda aka kafa a watan Agustan 2014, ya ce bayaga kyautatuwar rayuwa da suka shaida, akwai kuma karuwar kungiyoyin agaji na kasa-da-kasa da ke kai masu kayayyakin masarufi.

Wasu daga ‘yan gudun hijirar da suka share sama da shekara daya a sansanonin da aka hira da su, sun yaba da kamun ludayin Shugaba Buhari game yadda yake tunkarar kungiyar Boko Haram da kuma karin gudumawa da suke samu a daka da waje.

Malam Sa’ad Bello, shugaban hukumar kai daukin gaggawa ta kasa ta jahar Adamawa, ya ce an sami ingancin halin rayuwa a sansanonin ne sakamakon Karin kaso daga gwamnatocin Tarayya da na jahar Adamawa. Yana mai danganta karuwar kungiyoyin sa kai na kasa-da-kasa har da na cikin gida da samum tabbacin tsaron lafiya da suke da su, ganin irin galabar da sojojin Najeriya ke yi kan kungiyar Boko Haram - Sanusi Adamu

Ga cikakken rahoton daga wakilinmu Sanusi Adamu:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00


XS
SM
MD
LG