'Yan Gudun Hijira A Wasu Sansanoni A Jihar Borno Na Fama da Karancin Abinci

Wasu 'yan gudun hijira a jihar Borno

Wasu 'yan gudun hijira a jihar Borno na kokawa akan karancin abinci da magunguna da ababen bukatun yau da kullum lamarin da ya haifar da mace-mace cikin 'yan gudun hijiran.

'Yan gudun hijiran sun fito ne daga kananan hukumomi daban daban da rikicin Boko Haram ya rabasu da kauyukansu, kuma akasarinsu masu kananan karfi ne da suke dogara kan abun da gwamnati zata samar masu da zasu sa a baka.

To saidai tunda aka soma azumi 'yan gudun hijiran suka sake fadawa cikin wani halin kakanikayi na karancin abinci da magunguna lamarin da ya haifar da mace mace da dama.

'Yan gudun hijiran sun shaidawa Muryar Amurka yayinda wakilinta ya ziyarcesu, halin da suke ciki. Wani yace da ana basu abinci da safe da yamma amma yanzu sai daya ake basu, kuma da yamma kawai. Kawo yanzu mutane dubu daya da dari daya da hamsin suka rasa rayukansu a sansanin. Yawancin wadanda suka mutun yunwa ce ta kashesu.

Wata mata ta yi bayanin halin da take ciki da 'ya'yanta. Ta gayawa Muryar Amurka cewa zanin daya da take daurawa ne ta cire zata kai kasuwa ta sayar domin ta sayawa 'ya'yanta abinci.

Wani jami'in kiwon lafiya yace ana samun mace mace a sansanin amma yace cututtuka ne ke kashesu.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan Gudun Hijira A wasu Sansanoni A Jihar Borno Na Fama da Karancin Abinci - 4' 18"