Maharan da ba’a tantance iya adadinsu ba sun kai farmakin ba-zata kan karamar hukumar Damboa na jihar Borno da misalin karfe 6 saura yan mintuna na yamma inda suka kone gidaje da dama kamar yadda Aisha Kabu Damboa, 'yar asalin garin ta tabbatar mana ta wayar tarho.
Jami’an karamar hukumar garin Damboa da suka bukaci a sakaya sunansu sun tabbatar da aukuwan lamarin inda suka ce maharan sun kai farmaki ne da misalin karfe 5:34 na yammacin ranar alhamis.
Haka kuma, rahotannin farko-farko bayan harin daga wadanda suka shaida lamarin a yankin sun yi nuni da cewa maharan sun mamaye hedikwatar karamar hukumar da galibin mazauna kauyen damboa din ke zaune, inda suka rika harbin manyan bindigogi kan mai uwa da wabi.
Lamarin da ya tilastawa mutane tserewa don tsira da ransu tare da kulle kansu cikin gida yayin da maharan suka ci gaba da harbe-harbe a lokacin harin, in ji mazauna garin da suka nema kada a fadi sunansu.
Majiyoyi sun yi nuni da cewa tun da daren ranar Alhamis ne maharan da suka shigo garin da motoci akalla 8 suka fice, amma mutane na ci gaba da zaman zullumi a cikin gida saboda ba su san abin da zai iya biyo baya ba.
A halin yanzu dai rahotanni daga garin sun yi nuni da cewa mutane 6 ciki har da 'yan sanda uku, 'yar karamar yarinya daya, mace daya da kuma namiji daya suka rasa ransu.
Mazauna kauyen sun ce maharan sun kai hari kan ofis 'yan sanda na wucin gadi da ke garin inda suka kona motoci har guda uku.
Baya ga harin garin Damboa, maharan sun kuma kona ofisoshi da motar sintiri na rundunar hadin gwiwar kar ta kwana na JTF da na 'yan sa kai kan hanyar Biu in ji wata majiya.
Wannan harin na ranar alhamis shi ne karo na biyu a dikin mako 2 in ji mazaunan garin.
A saurari karin bayani daga bakin wani ganau da ya bukaci a sakaya sunansa.
Your browser doesn’t support HTML5