'Yan takarar kujerun majalisar wakilai da na dattawan Amurka a jam’iyyar Democrat na kara nuna damuwa game da yadda wasu masu kada kuri'a ke jefa ayar tambaya kan batun cewa shekarun shugaba Joe Biden na iya shafar wasu ‘yan takara a lokacin zabe, musamman a jihohi da gundumomi inda masu zabe ke kusan kan-kan-kan.
A cikin makonni uku tun bayan takon Biden a muhawarar ‘yan takarar shugaban kasa ta farko da aka yi, kokarin shawo kan shugaban dan shekaru 81 akan ya jingine batun neman takararsa na kara bayyana a fili. Yayin da kuri'un jin ra’ayoyin jama’a ke nuna Biden na bin bayan tsohon shugaban kasa Donald Trump a jihohi da dama da ke da muhimmanci wajen cin zabe, 'yan jam'iyyarsa na ci gaba da bayyana damuwarsu kan cewa yadda ya kasa tabuka abin kirki a wurin muhawarar na iya yin mummunan tasiri ga kokarinsu na ci gaba da samun rinjaye a majalisar dattawa da kuma samun rinjaye a majalisar wakilai.
Daga cikin masu bayyana damuwa a jam'iyyar shi ne Jon Tester daga jihar Montana, daya daga cikin 'yan majalisar dattawa a jam’iyyar Demokrat da masu kada ƙuri'a suka zaɓa a jihohin da galibi na ‘yan Republican ne. Tester, wanda ke neman wa'adi na hudu a Majalisar Dattawa, yayi kan-kan-kan da dan takarar jam'iyyar Republican Tim Sheehy a yakin neman zabe.
A shekaranjiya Alhamis, Tester ya ce ya na gani ya kamata Biden ya kawo karshen yakin neman zabensa.