Ibrahim Masari wanda Shugaba Tinubu ya nada shi mai ba da shawara kan siyasa a cikin sabbin mukaman mataimaka 14 da ya fitar, ya ce akwai wadanda ke karbar takardun kwarewar aikin mutane da yaudarar za su kai hukumar DSS da EFCC don tantancewar samun mukamai.
Ya bayyana cewa,“Mu na da rahoto ingantacce cewa akwai wadanda ke ta bi suna karbar kudaden mutane da takardun mutane cewa shugaban kasa ya ce su je su yi tantance mutane ko su zakulo mutanen da za a nada mukamai wannan magana ba gaskiya ba ne.”
Ku Duba Wannan Ma Jerin Sunayen Sabbin Ministoci A Yanar Gizo, Gaskiya Ko Farfaganda?Da ya ke magana kan wani jerin sunayen mutane da a ka fito da shi ranar litinin da ke nuna wadanda a ka nada ministoci da hakan bai tabbata ba, Masari ya ce masu gaggawa ne su ka aikata haka da kuma masu marawa wasu baya.
Babban dan siyasar gwamnatin Tinubun ya ce in Tinubu ya dawo zai bayyanawa duniya jerin sunayen ministocin ko kuma za a ji jawabi daga bakin sa.
Saurari rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5