Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ko Rana Daya Na Rike Takarar Mataimakin Tinubu Na Gode Allah-Ibrahim Masari


Ibrahim Kabir Masari
Ibrahim Kabir Masari

Mataimakin dan takarar jam’iyyar APC na shugaban kasa Ahmed Bola Tinubu wato Ibrahim Kabir Masari ya ce ko rana daya tak aka ba shi dama ya rike matsayin takarar ya gamsu.

Ibrahim Masari na amsa tambaya ne kan cewa an nada shi don rike kujerar ce kafin a nada ainihin wanda a ke son ya yi takarar.

Masari wanda tsohon sakataren walwala ne na APC ya ce amincewa da Tinubu ya nuna ma sa cikin jerin sunaye da a ka mika don ba da takarar mataimakin, na nuna ya gamsu da akidar sa a siyasa kuma ya zama abun yarda da zai ba wa marar da kunya.

A hirar shi da Muryar Amurka, Masari ya bayyana cewa, wannan karo musulmi-da-musulmi APC za ta yi a matsayin dan takarar shugaban kasa da mataimaki.

Mataimakin dan takarar ya ce la’akari da cancanta shi ya fi alheri ga ‘yan Najeriya maimakon bugewa da bambancin addin ko kabila.

Saurari hirar shi da Nasiru Adamu Elhikaya:

Ko Rana Daya Na Rike Takarar Mataimakin Tinubu Na Gode Allah-Ibrahim Masari
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:19 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG