BAUCHI, NIGERIA - A halin da ake ciki kuma, babu wani bayani game da sace wani basaraken kauyen Zira tare da dansa duk a karamar hukumar ta Toro da ke jihar Bauchi.
A ranar Asabar 18 ga watan Yuni ne dai aka sace tsohon sakatare janar din hukumar kwallon kafa ta Najeriya Alhaji Sani Ahmed Toro, wato Yeriman Toro.
Wata majiya kusa da iyalin Yariman ta nuna cewa masu garkuwa da mutanen sun bukaci a biya kudin fansa har naira miliyan dari da hamsin, ma’ana suna neman naira miliyan hamsin kan ko wane mutum daya.
A wata hira da Muryar Amurka, Abdulkadir Sani daya daga cikin ‘ya’yan Alhaji Sani Ahmed Toro, ya ce su na kokarin ganin mahaifinsu ya dawo gida. A halin yanzu dai addu’a su ke yi suna kuma fatan Allah ya dawo da shi lafiya.
Hukumomin tsaron jihar basu bada wani bayani ba game da lamarin, a cewar Abdulkadir.
A gefe guda kuma, hakimin garin Lame, wato sarkin yakin Bauchi, Alhaji Aminu Yakubu Lame, ya ce ya zuwa lokacin wannan rahoton ba su ji wani bayani ba daga mutanen da suka yi garkuwa da sarkin kauyen Zira, Yahaya Saleh Abubakar da dansa Habibu Saleh.
A daren jiya ne dai aka sace sarkin Lame da dansa a gidansu, a cewar Alhaji Aminu.
Saurari rahoto cikin sauti daga Abdulwahab Muhammed:
Your browser doesn’t support HTML5