Sarkin Kajuru Alh Alhasan Adamu wanda 'yan bindiga suka sace tare 'yar shi daya da jikoki da kuma wasu makwabta dai ya dawo shi kadai da yammacin yau litinin kamar yadda tsohon shugaban karamar hukumar Kajuru kuma sardaunan Kajuru, Alh. Abdurrashed A.A. Yaron Kirki ya tabbatarwa Muryar Amurka.
Ya ce dukkan al'umman Kajuru, musulmai da kirista sun nuna farin cikin dawowar sarkin gida cikin koshin lafiya kuma ba wani kudin da aka bayar. A ganin shi, yadda a ka yi wa masu garkuwan bayanin cewar sarkin bashi da lafiya kuma yana bukatar magungunansa, sannan bashi da irin wannan arzikin ya sa suka sako shi.
Wannan dai shine karon farko da 'yan bindiga su ka kutsa gidan sarki mai-daraja ta biyu kuma suka sace shi da wasu iyalan shi a jihar Kaduna, sai dai duk da dawo da sarkin kungiyar Dattawan Arewa ta ce akwai abun lura.
Karin bayani akan: Sarkin Kajuru Alh Alhasan Adamu, 'yan bindiga, jihar Kaduna, Kajuru, Nigeria, da Najeriya.
Dr. Hakeem Baba Ahmed mai-magana da yawun wannan kungiyar ya ce an bar harkokin tsaro ne suka lalace a Najeriya har ya kai ga yanzu, yara ba sa iya zuwa makaranta, matafiya basu tsira ba, har ya kai ga kan sarakuna.
Hare-haren 'yan bindiga a jihar Kaduna dai na kara hauhawa saboda baya ga daliban makarantu daban-daban da aka sace ko a jiya ma sai da 'yan bindigan suka kai hari garin Makarau Jankasa dake karamar hukumar Zangon Kataf inda al'umar yankin su ka ce an kashe mutane tara.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5