Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalilin Da Ya Sa Na Sauya Matsayata Kan Batun Sulhu Da ‘Yan bindiga - El Rufai


Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El Rufai
Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El Rufai

Cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan sha’anin yada labarai, Muyiwa Adekeye ya fitar a ranar Talata mai taken “mika wuya ga masu aikata manyan laifuka ba ita ce mafita ba”, El Rufai ya ce, idan kida ya canza rawa ma na sauyawa.

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai, ya maida martani ga masu sukar shi kan matsayin da ya dauka na kin yin sulhu da masu garkuwa da mutane.

El Rufai na fuskantar suka ne yayin da ragowar daliban kwalejin nazarin ilimin kula da dazuka ta Afaka da aka yi garkuwa da su, suka haura wata a hannun ‘yan bindigar.

Hakan kuma na faurwa ne a daidai lokacin da ‘yan bindigar suka kashe biyar daga cikin daliban jami’ar Greenfield da suka sace a kwanan nan.

Karin bayani akan: Goodluck Jonathan, ​Nasir El-Rufai, jihar Kaduna, Chibok, Shugaba Muhammadu Buhari, Kaduna, Nigeria, da Najeriya.

Maharan sun nemi a biya su naira miliyan 800 a matsayin kudin fansa kafin su saki daliban jami’ar.

Ita dai gwamnatin El Rufai, ta ce ba za ta yi sulhu ko ta biya maharan kudin fansa ba, abin da wasu ke ganin ya saba wata matsaya da gwamnan ya dauka a baya.

A lokacin da aka sace daliban makarantar Chibok a 2014, El Rufai, ya yi kira ga gwamnatin Goodluck Jonathan, da ta yi duk abin da za ta yi, domin kubutar da daliban – ciki har da tattaunawa da kungiyar Boko Haram.

Wani bidiyo da gwamnan ya yi wadannan kalaman a wancan lokaci, na nan yana ta yawo a intanet.

Sai dai cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan sha’anin yada labarai, Muyiwa Adekeye ya fitar a ranar Talata mai taken “mika wuya ga masu aikata manyan laifuka ba ita ce mafita ba”, El Rufai ya ce, idan kida ya canza rawa ma na sauyawa.

“Yana da kyau mutum ya yi amfani da basirarsa idan al’amura suka sauya. Ba zai yiwu a ce mafitar da mutum ya gabatar a 2014 ta zama ita ce maslaha ga wata babbar matsala da ta taso a yanzu ba.” Sanarwar ta ce.

“Tattaunawa da ‘yan bindigar bai samar da maslaha ba. A wannan zamani, muna amfani ne da matakin da ya fi dacewa da su.”

Sanarwar ta kara da cewa, yin garkuwa da dumbin mutane a shekarar 2014 bakon abu ne, amma al’amura sun sauya a yanzu, saboda bin matakin amfani da tattaunawa ba ya hana ‘yan bindigar ci gaba da ta’asar da suke yi.

“Dumbin kudaden da ake biya a matsayin na fansa idan ‘yan bindiga suka yi garkuwa da mutane, bai hana su sace mutanen ba, bai kuma sa sun rage ayyukansu ba ko ya tsorata su.” In ji Adekeye.

Matsalar satar mutane da ‘yan bindiga ke yi do neman kudin fansa ta zafafa a jihar Kaduna a ‘yan kwanakin nan, inda ‘yan bindigar kan kai hare-haren makarantu.

Hari na baya-bayan nan da suka kai, shi ne a jami’ar Greenfield da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, inda suka kwashe dalibai da dama.

Sai kuma garkuwa da suka yi da wasu ma’aikatan jinya biyu a babban asibitin karamar hukumar Kajuru.

XS
SM
MD
LG