Rahotanni daga jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya na cewa, ‘yan fashin daji sun sako karin daliban sakandaren Bethel Baptist High School su 15.
Jaridun Najeriya da dama sun ruwaito shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya reshen jihar Kaduna Rev. John Joseph Hayab wanda ya tabbatar da sakin dlaiban.
Sai dai babu bayanai da ke nuna cewa an biya kudin fansa ko akasin hakan. A baya, 'yan bindigar sun nemi a biya naira miliyan 60.
A karshen watan Yuli ‘yan bindigar suka sako dalibai 28 amma hukumomin makarantar sun ce ba a biya kudin fansa ba. Gabanin hakan wasu dalibai biyu sun yi nasarar kubuta.
Jaridar yanar gizo ta Daily Post ta ce a daren ranar Asabar aka sako daliban.
Sakin karin dalibai 15, na nufin akwai ragowar ‘yan makaranta 65 a hannun ‘yan fashin dajin.
A cewar Rev. Hayab, nan ba da jimawa ba, za a mika daliban ga iyayensu a cewar jaridar Tribune.
A ranar 5 ga watan Yuli masu garkuwa da mutanen suka far wa makarantar, wacce ke karamar hukumar Chikun, suka kwashe dalibai sama da dari.
Lamarin ya kai ga kisan sojoji biyu da ke gadin makarantar kamar yadda rahotanni suka nuna.
Kaduna ta kasance daya daga cikin jihohi da ke fama da matsalar masu garkuwa da mutane a arewa maso yammacin Najeriya, inda da farko lamarin ya fi rutsawa da matafiya.
Daga baya kuma lamarin ya yi kamari ya koma ana bin makarantu, inda akan sace daruruwan dalibai a shiga da su cikin daji.
A halin yanzu akwai daliban makarantar Islamiyyan Tegina sama da 100 da ‘yan bindigar ke rike da su a daji, wadanda aka yi garkuwa da su tun a watan Mayu.
Baya ga haka akwai daliban makarantar Yauri na jihar Kebbi da su ma suke hannun ‘yan fashin dajin baya ga daidaikun mutane da aka sace daban-daban a sassan arewa maso yammacin Najeriyar.