Wani mazauni kauyen ne ya shaidawa Muryar Amurka aukuwan lamarin da alkawarin cewa ba za a ambaci sunansaba.
A cewarsa, an kona masu gidaje lamarin da ya sa suka tsere daji da su da iyalansu, yana mai cewa ba su samu wnai dauki daga jami'an tsaro ba.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa DSP Sulaiman Yaya Guroje ya tabbatar mana da aukuwan lamarin amma ya ce sun samu izini daga kwamishinan ‘yan sanda kuma tuni rundunar sojojin jihar ta kai taimako.
Wani masanin tsaro kuma shugaban kungiyan stofin sojoji na arewacin Najeriya Malan Bashir Baba Yola ya ce rashin aiki ne yakan jefa al’umma ciki irin wannan mumunan hali.
A 'yan kwanakin nan wasu yankunan jihar ta Adamawa na shiga kangin mahara, wadanda kan far wa kauyuka su halaka mutane.
Karin bayani akan: ‘yan bindiga, ‘yan sandan, jihar Adamawa, Muryar Amurka, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.
Da sanyin safiyar ranar 9 ga watan Yuli wasu ‘yan bindiga da ake zargin mayakan Boko Haram ne, suka kai hari kan wani yankin Dabna da ba shi da nisa da garin Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha a jihar ta Adamawa, inda suka yi ta harbin kan mai uwa da wabi tare da kona gidaje.
Dabna gari ne da ya yi fice a harkar noma.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi Allah wadia da harin yana mai kira ga jami’an tsaronsa da suka tashi haikan.
A gefe guda, shi ma tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2019, Atiku Abubakar ya yi tir da wannan hari.
Saurari rahoto cikin sauti daga Salisu Muhammed Garba:
Your browser doesn’t support HTML5