Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Gari Sun Kona Wasu Yan Bindiga Kurmus A Jihar Edo


Rahotanni daga jihar Edo sun bayyana cewa, mutanen gari sun kona wasu mutane 5 da aka klama da makamai, wadanda ake zargin yan bindiga ne a kan hanyar Afuze-Uokha da ke karamar hukumar Owan ta kudu.

Majiyoyin sun yi nuni da cewa, yan bindigar su 5 sun aukawa matafiya da ke kan hanyar ta Afuze-Uokha ne, inda suka shigar da mutanen da suka yi garkuwa da su zuwa cikin daji daga bisani.

A cewar wata majiya daga yankin na Afuze-Uokha, ‘yan bindigar sun yi rashin sa’a daga bisani inda yan sa kai da aka fi sani da Vigilante suka kama su suka fito da su daga cikin dajin don kai su ga hukuma.

To sai dai a lokacin da mazauna yankin suka yi ido biyu da wadanda ake zargin, nan take suka kwace su daga hannun 'yan sa kan, suka kuma banka musu wuta tare da kone su kurmus har lahira.

Majiyar ta kara da cewa, yan bindigar sun kai na su farmakin ne suka shige a cikin daji ba tare sanin cewa yan sa kai sun sami labarinsu ba, daga bisani suka shiga dajin suka kuma zakulo su sannan suka gamu da ajalinsu a hannun gomman yan gari.

Wani shaidun gani da ido ya ce, 'yan garin sun fusata sosai suna cewa tura ta fara kaiwa bango, shi yasa suka dauki doka a hannunsu.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Kontongs Bello, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda yace rundunar ta fara gudanar da bincike kan lamarin kamar yadda jaridar ThisDay ta ruwaito.

Kontongs Bello ya kara da cewa 'yan sa kai sun fantsama cikin daji neman batagarin ne bayan samun labari kai harin da suka yi, tare da zakulo su kafin suka gamu da ajalinsu a hannun mutanen gari a yayin da yan sa kai ke kan hanyarsu ta kai mutanen ga hukuma .

Wannan ba shi ne karon farko ba da mutanen gari ke kwace 'yan bindiga daga hannun jami’an tsaro suna kashewa, don gudun abun da ka je ya dawo.

A cikin watannin baya-bayan nan ma sai da wasu matasa suka gudanar da zanga-zangar lumana a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna don neman gwamnati ta kawo karshen matsalolin tsaro suna cewa, tura ta fara kai bango.

XS
SM
MD
LG