Maharan sun afka garin, inda suka share kusan awa biyu suna sauke ruwan harsasai a cikin garin, suka kuma firgita jama'ar kafin su afkawa wani mutum bawan da suka sassare da adda bayan sun yi ta harbin sa ba tare da samun nasara ba.
Daya daga cikin mutanen garin ya ce, yana da kyau hukumomi su atallafa masu kasancewa a kowane dare, a wannan karamar hukumar mulkin ta Illela sai an dauke wani ko wata ko an kaiwa wani gari hari ko an kashe wani ko wata ko an yi garkuwa da mutane, wadanda sai an biga kudin fansa ake karbo su.
Jim kadan bayan ya dawo daga wurin ta'aziyar mutane biyu da a ka kashe a garin Kwandamo, shi ma suka kashe shi tunda, maharan sun hadu ne da daya daga cikin ‘yan bangan garin bayan sun kashe wannan magidancin da suka sassare, a cewar shugaban karamar hukumar mulkin Illela Injiniya Aliyu Salihu.
Su dai maharan, sai da suka dauki wani bawan Allah daga Gari Mai Ruwa kamin su afkawa garin Kwandamo, kuma bayan kwana guda da ya gabata wadansu maharan sun kai hari a Sonani inda suka dauke wani mutum guda.
Saurari rahoto cikin sauti daga Harouna Mamane Bako:
Your browser doesn’t support HTML5