'Yan bindigar dai sun auka garin na Beri ne dake yankin karamar Hukumar Mariga da sanyin safiyar Litinin, inda bayanai su ka nuna cewa sun share sa’o’i uku suna tabka gumurzu a tsakaninsu da mutanen gari da 'yan banga da kuma wasu jami’an tsaro.
'Yan bindigar sun kashe babban malamin garin mai suna Malam Bello Beri tare da kona karamin ofishin 'yan sanda na garin.
Karin bayani akan: Beri, 'Yan bindiga, Jihar Neja, Jihar Nejan, Nigeria, da Najeriya.
Gwamnatin Jihar Neja ta tabbatar da kai harin amma tace bata da tabbacin adadin mutane da aka kashe, inji Sakataren Gwamnatin Jihar Nejan Alh. Ahmed Ibrahim Matane.
Har ya zuwa lokacin hada wannan rahoton dai babu wani karin haske daga rundunar 'yan sandan Jihar Neja.
Saurari cikakken rahoton a cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5