‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Da Dama A Mali

MALI

Sama da fararen hula 20 ne aka kashe a wani hari da aka kai a tsakiyar kasar Mali a ranar Asabar, kamar yadda wani jami'in yankin ya fada a ranar Lahadi.

WASHINGTON, D. C. - An kai harin ne a wani kauye da ake kira Circle of Bankass a yankin Mopti, daya daga cikin yankuna da dama a arewacin Mali kuma a tsakiya inda kungiyoyin masu da'awar jihadi da ke da alaka da Al Qaeda da IS ke kaddamar da hare-haren ta'addanci tun shekara ta 2012.

Magajin garin, Bankas Moulaye Guindo ya ce wasu da ba a san ko su wane ne ba ne suka kai farmaki kan mutanen kauyen a kan hanyarsu ta zuwa aikin gonakinsu.

“A jiya mun kirga mutuwar mutane 19 amma a yau sun zarce 20,” in ji shi ta wayar tarho.

Rikicin kasar Mali dai ya samo asali ne a lokacin wani boren Abzinawa a shekarar 2012 wanda tun daga lokacin ya yadu a yankin Sahel da kuma arewacin kasashen yammacin Afirka.

Mayakan jihadi sun samu galaba duk kudaden da sojoji ke kahsewa don fatattakar mayakan inda suka kashe dubban mutane tare da raba miliyoyi da muhallansu, yayin da suke kai hare-hare kan garuruwa, kauyuka da wuraren da sojoji suka yi musu hari.

Gazawar hukumomi na kare fararen hula ya taimaka wajen juyin mulki sau biyu a Mali, daya a makwabciyarta Burkina Faso da kuma daya a Nijar tun shekara ta 2020.

-Reuters