Kakakin rundunar ‘yan sandan Filato, Alfred Alabo, ya ce an kai hare-haren ne da sanyin safiyar Alhamis, inda wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka kai hari kauyen Tagwam Lawuru, inda suka harbe mutane 17 suka kashe wasu uku a kauyen Layowok da ke kusa.
“Sakamakon hare-haren, wasu mutane da dama sun samu raunuka daban-daban na harbin bindiga,” in ji Alabo a wata sanarwa da ya fitar, inda ya bukaci a kwantar da hankula tare da yin alkawarin kamawa tare da hukunta wadanda suka aikata laifin.
Yawan tashe-tashen hankula a yankin, ya samo asali ne daga kabilanci da addini tsakanin Fulani makiyaya Musulmai da manoma Kiristoci.
Sai dai masana da ’yan siyasa da dama sun ce sauyin yanayi da fadada noma na haifar da gasa ga filaye da ke jefa manoma da makiyaya cikin rikici ba tare da la’akari da addini ko kabilanci ba.
~ REUTERS