A sanarwar da ta aikawa kafafen yada labarai a cikin daren jiya lahadi ma’aikatar tsaron jamhuriyar Nijar ta ce wata bataliyar dakarun tsaro mai sansani a kauyen Fantio ta yi kicibus da daruruwan ‘yan ta’adda a lokacin da take kokarin tantance wasu bayanan dake cewa an hango tarin ‘yan bindiga akan babura suna kokarin afkawa kauyen na Fantio.
A ranar asabar din da ta gabata, an kwashe lokaci mai tsawo ana fafatawa a tsakanin wadannan barade da ‘yan ta’adda lamarin da ya ba sojojin gwamnati damar karkashe gomman ‘yan ta’addan tare da kwace masu na’urorin sadarwa da kuma lalata baburansu da dama.
Jigo a kungiyar Suavons le Niger Salissou Amadou ya jinjinawa sojan Nijar saboda yadda suka yi tsayin daka wajen kare martabar kasa da al’umar ta.
Yawan wadannan mahara ya taimaka masu har suka yi nasarar kashe sojoji 12 tare da jikkata wasu 8 inji wannan sanarwa wacce ta kara da cewa daukin da aka samu daga sojan garin Wanzarbe da Tera da iragen saman da suka rika shawagi ya sa ‘yan bindigar suka tsere suka bar gawarkakinsu da dama yashe a kas.
Koda yake sun arce da wasu daga cikin mutanen da aka kashe masu, tsohon shugaban kwamitin tsaro a majalisar dokokin kasa Hon. Hama Assa ya nuna juyayi akan rasuwar jami’an tsaro ya kuma gargadi jama’ar Nijar a maida dukkan wani bambance-bambance don tunkarar kalubalen tsaro.
Kauyen Fantio na karkarar Gorouol dake gundumar Tera a jihar Tilabery na daga cikin garuruwan da hukumomi suka girke wa sojoji takanas a farkon shekarar nan domin kare jama’a bayan la’akari da yadda ‘yan ta’adda suka addabi garin da kewaye a can baya.
Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5