'Yan Bindiga Sun Fara Karbar Haraji a Wasu Kauyukan Sakkwato

Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal

A wani al'amari mai kama da nuna isa da tsabar rashin tsoron hukuma, 'yan bindiga sun fara sa haraji a wasu kyauyukan Sakkwato.

Matsalar rashin tsaro na ci gaba da ta'azzara a wasu yankunan jihar Sakkwato, inda yanzu har ‘yan bindiga sun fara sa ma wasu daga cikin kauyukan haraji tare kuma da ci gaba da kai hare hare ma wasu kyauyukan.

Bayan da aka ga kamar kura ta lafa a yankin gabashin Sakkwato, sai gashi ‘yan bindiga sun waiwayo da wata sabga ta aza wa mutane haraji musamman ma a karamar hukumar Isa.

KANO: Masu sace mutane da 'yansandan Kano suka cafke a dajin Falgore

Bashir Altine Guyawa shugaban rundunar adalci ta jihar Sakkwato kuma mazaunin yankin na Isah, ya ce yanzu sace mutane ya ma fara zama tsohon yayi. Sa haraji ake yi tare kuma da kora dabbobin mutane, ta yadda har shanun noma na kyauyawan an yi awon gaba da su.

Har wayau a cikin wannan makon yan bindiga sun yi dirar mikiya a wani kauye mai suna Dayiji cikin karamar hukumar Gudu dake arewacin Sakkwato inda suka bankawa garin wuta.

Wannan harin dai jama'ar garin, ta bakin wakilinsu a Majalisar Wakilai ta Najeriya, Yusuf Isah Kurdula su na ganin harin ramuwar gayya ne. Ya ce kwanan baya mutanen yankin sun yi nasarar damke miyagun da dama su ka kuma mika su ga hukuma.

Rundunar 'yan sanda ta tabbatarda aukuwar wannan harin kamar yadda kakakin rundunar ASP Muhammad Abubakar Sadiq ya tabbatar, inda ya ce maharan sun kai kimanin goma sha biya.

ZAMFARA: Mutanen da aka yi garkuwa dasu

Har wayau, duk a cikin wannan makon ne, wasu mutane da ba a san ko suwaye ba suka hallaka wani dan kasuwa dan kabilar Igbo mai suna Obinna, mazaunin unguwar Sabaru a Sakkwato.

Rundunar 'yan sanda Sakkwato ta ce tana daukar matakai domin shawo kan matsalar rashin tsaron.

Ga Muhammadu Nasir da cikakken rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan Bindiga Sun Fara Sa Haraji a Sassan Sakkwato


'