'Yan bindigar sanye da dogayen rigunan abaya sun yi awon gaba da mutane 26 galibinsu mata da kananan yara a harin da suka kaiwa garin Runka dake karamar hukumar Safana ta jihar Katsina.
Wata majiya a garin ta shaidawa tashar talabijin ta Channels ta wayar tarho a yau Litinin cewa 'yan bindigar sun mamaye yankin ne a daren Asabar din da ta gabata da misalin karfe 10, inda yace maharan sun yi ta harbin kan mai uwa da wabi a sassa da dama na garin.
"Yan bindigar basu illata kowa ba in banda mutum guda wanda suka harba tare da raunatashi bayan da yayi kokarin arcewa. A yanzu haka da nake magana daku an kwantar dashi a asibiti.
"Sun sace akalla mutane 25 saboda ko a cikin dangina an sace mutane mutane 12."
"A yayin harin an ji daya daga cikin 'yan bindigar a wata hira da wani da ba'a san ko wanene ba ta wayar tarho na cewar, "yau gamu a garinku."
Har yanzu hukumomin 'yan sandan Katsina basu ce uffan akan batun ba kasancewar kakakin rundunar jihar Abubakar Sadiq bai yi martani ga tambayoyin da tashar talabijin ta Channels ta yi masa ba.
Sai dai Shugaban karamar hukumar Safana Abdullahi yace anyi garkuwa da mutane 22 amma wasu sun samu sun gudu daga hannun maharan.