ABUJA, NIGERIA - Da farko da ‘yan bindigar sun je yankin Kau inda suka yi awon gaba da wasu mutane masu yawa da wasu alkaluman ke cewa sun haura mutum ashirin, daga bisani kuma suka shiga garin na Bwari inda suka sake awon gaba da wani mutum da yaransa mata shida.
Muryar Amurka ta kai ziyara sau biyu a yankin da abin ya faru inda ta yi kokari samun tattaunawa da iyalan wadanda abin ya faru da su, amma sun ki yin magana bisa halin firgici da suke ciki.
Wani ganau da abin ya faru a gabansa ya shaidawa Muryar Amurka cewa ‘yan bindigar da suka shiga garin Kau, shun sace dan hakimin garin da sabuwar amaryarsa da kuma wani dan siyasa da iyalansa goma, ciki har da yaransa biyar da matansa.
Ko da yake daga bisani sun sako shi akan cewa ya je ya hado masu Naira milyan ashirin a matsayin kudin fansa, da babura biyu da kayan abinci dangin shinkafa, wake da taliya.
A gefe daya kuma su ma ‘yan bindigar da suka kama wani Alhaji Mansoor da iyalansa, shi ma sun sako shi inda suka nemi ya harhado masu Naira milyan sittin don fansar yaransa da dukkanninsu mata ne su shida.
Dan jinkirin da aka samu ba'a kawo kudin ba ya sa har sun bindige daya daga cikin ‘yan matan mai suna Nabeeha a matsayin wani gargadi don su nuna da gaske suke yi.
Hedikwatar rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce tana iya bakin kokarinta wajen ceto mutanen cikin aminci.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya ACP Muyiwa Adejobi, a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai ya ce tuni suka fara tsara aikin ceton, amma yayi gargadin cewa aikin na cike da sarkarkiya don haka dole ne ayi taka-tsantsan.
ACP Adejobi ya ce aikin zai kunshi ceto duk mutanen da aka yi garkuwa da su sannan a tsara yadda za'a hana aukuwar haka nan gaba.
Karamar hukumar Bwari dai na yamma maso kudancin birnin Tarayya Abuja ne da ta hada iyaka da jihohin Kaduna, Naija da Nassarawa, abin da ya sa masana ke cewa ‘yan ta'addan da ka can ne suke kawo hari a yankin.
An yi yakinin cewa kasancewar yanayin yankin ya zo daidai da na sauran jihohin da ta ke makwantaka da su na manya-manyan duwatsu da manyan dazuzzuka, ya na taimakawa ‘yan bindigar wajen samun saukin tafka ta’addancinsu.
Saurari cikakken rahoto daga Hassan Maina Kaina:
Your browser doesn’t support HTML5