Yan adawa a majalisar dokokin nijer sun ki halarta bude bukin wani zaman taron da majalisar dokokin kasar da aka fara a dazu dazun nan domin duba kasafin kudin kasar na sabuwar shekara mai kamawa.
Ko bayaga rashn halartar yan adawar ana shi zaman majalisar ne a wannan karon ba tare da shugaban majalisar ba inda yanzu hakan yake ci gaba da gudun hijira a waje.
A baya dai rikici ya barke kan batun hurumin kiran taron inda daga wurin gudun hijiar sa shugaban majalisar yace ya kira taron a ranar laraba 7 ga wannan watan, wanda su kuma bangaren masu rinjaye suka ce ko kadan, taron za’a bude shi ne a ranar yau 1 ga watan Octoba.
Sai dai kuma wani abu da ba’a taba yi ba a tsawon tarihin Majalisar Dokokin Nijar, shine zama ba bare da kakakin majalisar ba, wanda a halin yanzu shine Mallam Hamma Amadou.
Shi dai Hamma ya share tsawon shekaru uku yana jagorancin wannan majalisa, tare da bude taro harda jawabai, wadanda wani lokacin ke sukar manufofin shugaban kasa Mahamadu Issoufou.
Larabannan, mataimakin shugaban majalisar dokoki Ben Umaru Mahamadu shine ya jagoranci bukin bude majalisar dokokin wanda ya bayanna cewa ana taron ne yau ba tare da shugaban majalisar dokoki ba.
Your browser doesn’t support HTML5