Mai sharia Bukar Sani Ibrahim, na jamhuriyar Nijar, yace ana sauraren sakamakon karar da shugaban majilsar kasar Nijar, Hamma Amadou, ya shigar.
Wanda idan har sakamakon bai baiwa shugaban majalisar gaskiya ba, ana iya yi masa sharia, ko baya nan.
Kuma dag bisani alkali na iya bada samaje domin kamashi a duk inda ya kasance, kuma kotu jamhuriyar Nijar, da hadi gwiwar hukumomi tsakanin kasa da kasa na iya sa samajen kamo sa, domin zartar da hukumcin da alkalin ya yanke a kansa.
Kasar Burkina Faso, dai inda shi shugaban majalisar, yake a yanzu akwai yarjejeniyar ta fanin sharia tsakanin ta da jamhuriyar nijar.