shuwagabannin sun ja hankalin yan siyasar da su shirya tsakanin su saboda wasu matsalolin da kan iya tasowa. Ustazu malam Haja limamin Masalacin majalisar dakokin kasar,inda yake daya daga cikin dandalin da ake tabka mahauwara mai zafin gaske.
Irin mahauwaran da ta haddasa jayyaya tsakanin masu rinjaye da masu hamayya a kasar ta Nijer.
Limamin cewa yayi ”Magana dake garemu a matsayin mu na masu karantawa Allah yace Manzon Allah yace abunda zamu shawarcesu dashi, shine sun jin tsoron Allah su neme abunda sais a kasar nan ta ci gaba su barwa baya gado mai kyau, basu bar rigimar da muke gani ba, wannan baya kai kasa gaba.”
Shi kuwa babban limamin mabiya addini krista cewa yayi ”ko da yake mu dauki magana ne inda akayi laakari da halin da Kasar Nijer ke ciki a fanita na siyasa kasar na cikin wani hali mai ban tsoro."
Wannan ba shine karo na farko ba da shuwagabanin addinai ke yin kira ga ‘yan siyasar kasa domin jagorancin kasar cikin tsanaki batare da haifar da rigingimu ba irin na siyasa.